Wani babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran wato IRGC ya yabawa ma’aikatan kasar kan hakurinsu a tsakiyar takunkuman tattalin arziki mafi muni wanda gwamnatin kasar Amurka da kawayenta suka dorawa JMI.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Birgedia Janar Hassan Hassanzadeh yana fadar haka ya kuma kara da cewa ma’aikata duk tare da takurawar rayuwanda da suke da suke ciki, saboda takunkuman tattalin arzikin Amurka.
Yace ma’aikata sun ci gaba da samar da kayakin da ake bukata a cikin gida duk tare da takunkuman tattalin arziki masu tsanani da aka dorawa kasar. Kumawannan tsayawarsu daram ya taimaka ya kuma rage radadin da takunkuman.
Janar Hassanzadeh ya bukaci Majalisar dokokin kasar ta taimakawa ma’aikata don samar da daidaito a kasuwannin kasar. Ya ce duk tare da matsin lamba ma’aikata musamman na kamfanoni masu samar da bukatun yau da kullum sun ci gaba da ayyukansu duk tare da karancin albashi wanda baya isarsu biyan bukatunsu na yau da kullum.
Brigadier General Hassan Hassanzadeh, dai shi ne babban kwamandan rundunar Mohammad Rasoolullah da ke Tehran babba, kuma ya je majalisar dokokin kasar Iran dake nan Tehran don sanya ido a kan yadda take gudanar da ayyukanta musamman kan abinda ya shafi rayuwar ma’aikata.