IRGC Ta Musanta Labarin Tattaunawa Da Trump Ta Bayan Fage (DUPLICATE)

IRGC ta musanta ikirarin Shugaba Donald Trump na cewa Amurka na tattaunawa da dakarun ta bayan fage, tana mai jaddada cewa babu wata tattaunawa a

Kakakin dakarun kare juyin juya halin musulunci (IRGC) ya musanta labarin da ke cewa Amurka na tattaunawa da su ta bayan fage.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Brigadier General Hossein Mohebbi  yana fadar haka, ya kuma kara da cewa riyawar Trump kan cewa Amurka na tattaunawada  dakarun na IRGC ba gaskiya bane, kuma wannan wata alama ce ta shank aye a wannan yakin wanda Amurka ta yi.  Ya ce babu tattaunawa da Amurka a bayyane ko a boye.

Mohibbi ya kara da cewa, shugaba Trump yana irin wadan nan maganganun ne don ya kwantarwa Amurkawa rai, saboda musubin da ya sa su a ciki, na fara yakin da ya kasa kawo karshensa.

Har’ila yau yana haka ne saboda ya zama yana da iko kan yanda farashin man fetur yake tashi ya kuma fadi a kasuwannin duniya.

Yace kasar Iran tana da cikekken iko a kan mashigar ruwa da harmuz, kuma babu wani jirgin da yake wucewa a mashigar ba tare da umurnin Iran ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted