213-Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a)

213-Assalamu alikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmi na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

213-Assalamu alikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmi na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////…Madallah, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma sirar Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (s) dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo mako, a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku ziyarar Imam Al-Hassan (a) zuwa kasar sham da kuma mahawarorin da yayi da mu’awiya dan Abusufyan da mutanensa.

A cikin shirimmu da ya gabata munji yanda Mu’awiya ya kodaitar da Abdullahi dan Zubair ya kalubalanci Imam Al-Hassan(a), yayi alfakhari da matsayin babansa a musulunci da kuma dangantakarsa da banu Hashin ta  mahaifiyarsa Safiyatu diyar Abdulmuttalib. Sai Abdullahi ya amince, ya kuma kwana yana tunanin abinda ya zai fadawa Imam Al-Hassan (a) idan sun hadu a fadar Mu’awiya.

A lokacinda suka hadu sai Abdullahi dan Zubair ya tashi, ya fara aibata Imam Al-Hassan,(a) kan yanda ya mikawa Mu’awiya shugabancin al-ummar musulmi ba tareda an yi yaki ba. Sai ya ce masa hakan wata alama ce ta rauninsa (a) da kuma tsoro, duk da cewa an san mahaifinsa Imam Ali(a) da jarunta amma shi bai gajeshi ba.

Sannan ya koma yana yabon kansa yana cewa, da shi ne ya sami abinda Imam Al-Hassan ya samu da sai ya nunawa duniya kan cewa dan Zubair dan awwam ne, dan kuma safiyyatu diyar Abdulmuttalib.  Ba zai ji tsoron yaki ba kuma da ba zai ji tsoron mu’awiya ba. Sai ya zauna. A lokacinda ya zauna sai Imam Al-Hassan (a) ya shi ya bashi amsa yana cewa:

{..Na rantse da All..idan ba don kada banu umayya su jingina mani gazawa a Magana ba, da na wadatu da yin shiru saboda wulakanta ka. Sai zai bayyana maka cewa, ni ba gajiyayye bani, kuma ba wanda baya iya Magana bane. Ni kake aibawa ? sannan ni kake alfakhari a kaina?.

To kasan cewa kakanka (Awwam) bai da gida a jahiliyya don haka bai da daukaka, don haka matarsa wato kakata Safiyyatu diyar Abdulmuttalib ce, (ta daukaka shi) shi kuma yayi alfakhari a kan larabawa da samun aurenta, saboda daukakatar ta, ta yaya kai Abdullahi zaka yi alfakhari da wacce ita wasila ce ga daukakarka, shuwagabanninta ne masu daukaka,  kuma mune mafi daukakar mutane.. muna da daukaka mai haskakawa, da kuma karamci mai rinjaye.

Sannan ka riya cewa, na mika Mulki, ta yaya haka zai kasance, kaiton ka? Al-hali ni ne dan mafi jarunta daga cikin larabawa, kuma Fatima shugaban matan duniya ce ta haife ni? Mafi alkhairin kuyangun All..? ban aikata haka ba, saboda tsoro da Rauni ba, sai dai irinka ne suka yi mani bai’a, suna nemata saboda kwandala, yana mani karya da soyayya a baka, ni ban amince da taimakonsa ba, don ku yan gidan mayaudara ne, ta yaya haka ba zai kasance kamar yanda na fada ba? Hakika babanka ya yi bai’a wa Amirul muminina(a) sannan ya kwance bai’arsa, ya juya baya ta duga dugansa, ya yaudari wasu daga cikin sahabban Manzon All..(s) don ya batar da mutane, a lokacinda ya kusanci linaman, ya ga hasken takubba, sai ya wuce ya je inda aka kashe shi a banza bai da mataimaki, kai kuma aka zo da kai a dabaibaye, a matsayin fursinan yaki, hakika dabbobi sun tattakaka da kafafuwansu, haka ma dawakai, sai Malik dan Ashtar ya sami iko a kanka, sai ka shaku da yawunka, sai ka fadi a kan kafafuwanka, kamar kare idan ya ji tsoron zakoki.

Mu kuma, Kaitonka, haske ne ga kasa da sassansa, al-ummu suna alfakhari da mu,  kuma jagorancin al- amura suna garemu,  shin kana yunkuri al-hali kana yaudarar mata? Sannan kana alfakhari a kan Yayan annabawa? Har yanzun ana karban zancemmu, ana kuma mayar da zancenka da na mahaifinka.

Mutane sun shiga addinin kakana wasu da sonsu, wasu kuma a dole, sannan suka yi bai’a wa Amirulmuminina (a) sannan ya fita zuwa ga talha da babanka a lokacinda suka kwance bai’arsu suka kuma yaudari matar manzon All..(s), sai aka kashe babanka da Talha, sannan aka kawoka a matsayin fursinan yaki, sai ka yi ikrari da zunubanka ka rokeshi da dangantakarku da shi kada ya kashe ka, sai ya gafarta maka, don haka kai yentaccen bawan mahaifi nane, ni shugabanka ne kuma shugaban babanka ne, ka dandane sakamakon ayyukanka }.

Daga nan sai Abdullahi dan Zubair ya ji kunya, ya kuma yi nadamar abinda ya aikata, sai ya zo wajen Imam Al-Hassan (a) yana lallashinsa, yana neman afwarsa, yana cewa mu’awiya ne ya dulmuya shi cikin abinda ya aikata.

Ya ce: Ina neman uzurinka ya baban Muhammad, wannan nqe ya bukace ni in yi muhawara da kai (yana nufin Mu’awiya}. Ina neman afwanka bayan jahilcin da na aikata, lalle ku Ahlulbaiti hakuri dauriya suna daga cikin halayenku.

Sai Imam (a) ya juya wajen Mu’awiya yana cewa:

{Ka duba! shin ka ga gazawa wajen muhawara da wani? Kaitonka! shin ko ka san daga wani gida na fito?. Su waye ne iyaye na? don haka ka kula! Kafin in shifantaka da shifa wacce matafiya za su tafi da shi zuwa ko ina duniya.}

Sai dan Zubairu yace: Ya cancanci haka. Sai Mu’awiya ya juya wajen dan Zubair yana cewa: Amma na rantse da All..ya yaye mani abinde ke zuciyata dangane da kai, ya yi jifa ya kuma kashe ka. Ka zama kamar abin wasa a hannunsa yana ta wasa da kai. Ina fatan ba zan sake ganinka kana alfakhari da wani ba har abada.

Wannan kadan kenan daga tafiyar Imam Al-hassan(a) zuwa kasar Sham, tafiya ta farko, a cikin wannan tafiyar, Mu’awiya ya kasance cikin tsoro da fargaba, saboda yana jin tsoron Imam (a) yana iya dagola masa al-amura ko kuma ya haddasa wani yaki a tsakaninsu.

Bai manta da abinda ya faru a yakin Siffin ba, ya san cewa mahaifin Imam Al-Hassan ya sami cikekken nasara a kan mutanen sham, idan ba yaudara da kaidin da suka kulla don raba kan mutanen Iraki ba da ya san cewa ya gama yawa.

Don haka a duk lokacinda Imam Al-Hassan (a) ya shigo wajensa yana taka tsantsan da shi, sannan idan wasu daga cikin mutanensa sun aikata wani abu wanda bai dace ba yakan kobesu, don kada ya zama fitina.

Malaman tarihi sun bayyana cewa, wata rana Amru dan Uthman dan Affan ya shiga jayayya da Usama dan Zaidu dan Haritha maulan Manzon All..(s), sun shiga jayayya kan mallakan wani fili a tsakaninsu a gaban Mu’awiya dan Abu sufyan.

Jayayya ta yi tsawo har sai da Usama dan zaidu y afara barazana ga Amurka kan cewa zai nemi taimakon Hashimawa, sannan ya tashi ya je ya zauna a kusa da Imam Al-Hassan wanda yake wurin. Sai sauran Hashimawa a wurin suka tashi suka zo suka zauna kusa da su.

A lokacinda umayyawa suka ga haka sai suma suka zo suka zauna kusa da Amru dan Usman, suka taru kusa da shi. A lokacinda Mu’awiya ya ga haka, sai ya ji tsaron fitina, don haka ya shiga don kawo karshe husumar. Sai ya zo ya ce masu. Kada ku yi gaggawa, ni naga lokacinda Manzon All..(s) ya bawa usama dan zaidu wannan filin da kuke jayeyya. Don haka Mu’awiya ya yanke hukuncin cewa usamane yake da gaskiya. Ya fifiya shi a kan Amru dan Usman.

A lokacinda Hashimawa tare da Imam Al-hassan (a) suka fita daga fadar, sai umayyawa sun shiga wajen mu’awiya suna kukan yanda ya hukunta wa Usama mallakar wannan filin ya bar Amru da Uthman. Sai mu’awiya ya basu amsa da cewa yana jin tsoron kada fitina ta shi a sham.

Yana cewa ku barni, wallahi ba zan manta da idanunsu karkashin itatuwan magafir a siffin ba, sai hankali na ya tashi. Sannan ku san cewa farkon yaki yana faraway ne da cacan baki, sannan tsakiyarsa kararraki da aibata juna sannan karshen sa masiba.

Sai ya kawo waya kasidar Imru kai dangane da haka. Sai ya kara da cewa, abubuwan da suke cikin zukata ne suke  girma su zama yaki, al-amari kadan yana hana wani al-amari babba.

Da wannan kuma muka kawo karshen ziyarar da Imam Al-Hassan (a) ya kai kasar Sham bayan ya mika shugabancin al-ummar musulmi ga Mu’awiya dan Abusufyan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted