Gwamnan babban bankin kasar Iran Dr Abdunnasir Himmati ya gana da firay ministan kasar Iraki Ali Al-Zaidi inda bangarorin biyu suka tattauna al-amura da suka shafi tattalin arziki da kudade a kasashen yankin.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya bayyana cewa a taron tare da Fray ministan kasar Iraki, a birnin Bagdaza, Gwamnan babban bankin kasar Iraki, Muhammad Kazim Ale Sadiq jakadan kasar Iran a Iraki da wasu jami’an babban bankin kasashen biyu sun halarci taron.
A bangarensa Ali Al-Zaidi Fray ministan kasar Iraki ya ce a halin yanzu gwamnatinsa tana kokarin maida kasar Iraki a matsayin cibiyar hada hadan kudade a kasashen yankin. Ya kuma bayyana damuwarsa da yawan matsalolin hada hadar kudade wanda kasashen yankin suke fama da su.
Al-Zaidi ya kammala da cewa samun tabbataccen zaman lafiya a yankin yana daga cikin al-amura masu muhimmanci don samun ci gaba a tattalin arziki kasashen yankin.
A wani bangare kuma Jami’an gwamnatocin kasashen biyu sun tabo maganar harkokin kasuwanci tsakanin kasashen Iran da Iraki da kuma batun fadadasu, har ila yau da batun dawo da wasu kudaden JMI da sukamakale a kasar ta Iraki saboda kafar ungulun da Amurka take yi a cikin al-amuran kasashen biyu.
Kafin haka Dr Himmati ya gana da gwamnan babban bankin Iraki da kuma ministan kudade da kasuwanci na kasar.