Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghaei ya bayyana cewa, hare haren da aka kaiwa ofishin fray ministan yankin Kurdistan na kasar Iraki Masrur Barazani wata dasisa ce ta bata dangantaka tsakanin kasashen Iran da Iraki.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Baghaei yana fadar haka a jiya Litinin ya kuma kara da cewa, harin na ranar litinin 17 ga watan Augusta, akwai alamun wasu makiya ne suke son shiga tsakani don gwara kan kasashen biyu.Don haka ya bukaci a gudanar da bincike don gano wadanda suke da hannu a cikin wadannan hare hare,musamman wadanda suke da dangantaka da wasu kasashen waje a yankin.