Kakakin gwamnatin kasar Iraki ya bada sanarwan cewa gwamnatin kasar Iraki tana gaggauta shirin karban iko da al-amuran tsaron kasar Iraki daga hannun rundunar kwance masu fada da kungiyar Daesh karkashin jagorancin Amurka a kasar.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto tashar talabijan ta Al-Mayadeen tv, wacce ta nakalto Haidar Abbodi kakakin gwamnatin kasar yana tabbatar da haka a jiya litinin.
Abbudi ya kara da cewa, yana kokarin gaggauta karban iko da harkokin tsaron kasar daga kawancen kasa da kasa nan da karshen watan Satumba mai zuwa, Al-Amuran makamai da tsaro zai zama karkashen cikekken ikon fray ministan kasar. Daga lokacinda kuma ba wata kasa daga waje wacce zata mallaki makamai a cikin kasar Iraki.
Abbudi, ya kara da cewa daga ranar 30 ga watan Satumba mai zuwa fray ministan kasar Dr Ali Azzubaidi ne kawai babban kwamandan sojoji da Jami’an tsaron kasar Iraki gaba daya.