12-Al-Adu Da Ci Gaban Addinin Musulunci A Tarihi

12-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Al-adu da ci gaban addini addinin musulunci a tarihi, wanda

12-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Al-adu da ci gaban addini addinin musulunci a tarihi, wanda ni tahir amin yake kawo mako sau guda a ko wani mako. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun tsaya inda muka yi magana dangane da yanda aka fara tarjama ilmin kasashen girka masar da india zuwa harshen larabci a cikin daular ambasiyawa, bayan an sami wadatuwar masana’antun takarda a kasashen musulmi.

Kafin haka mun bayyana cewa musulmi sun fara samar da masana’antun buga takardu ne a cikin karni na 3 bayan hijira, a birnin samanaqanda, bayan da aka kama wasu mutanen China a yaki da musulmi a kasar Kazakist aka kawosu samarakanda suka kafa masana’antar samar da takardan rubutu. Daga nan sai ya wasu zuwa Bagdaza, zuwa shamad wadanda suka hada da Tripoli na kasar Lebanon da damascus da sauransu. Sannan wannan ya yadu zuwa kasashen arewacin Afirka, sannan ya tsallaka zuwa Aspania a birnin Qodova na kasashen Turai.

A hankali a hankali, ya yadu zuwa, sauran kasashen turai wadanda suka hada da italia da Jamus, faransa sannan ingila.

Sannan mun ji yanda aka tarjama’ littafan kasar girma kama daga ilmin likitanci, madiki da falsafa, da ilmin taurari da geographiya da tsirrai da sauransu zuwa harshen larabci.

Malaman musulmi sun tarjama ilmomi da dama, har sai da ya kai sun bude makarantu manya manya a kasashen musulmi, musamman a birnin Bagdza. Aka fara koyarda dukkan wadannan ilmomi, aka kowa kawo ci gaba a cikinsu.

Musulmi suka sana manya manyan malaman girka wadanda suka hada da Aflatun, Fithagurth, Arosto dasauransu.

Sannan mun fara maganar ilmomin da aka tarjamasu daga kasar Indiya ne sai lokaci ya kure mana.

Mun bayyana cewa wasu daga ilmomin da suka shiga cikin wayewar addinin musulunci a tarihi sun fito ne daga kasar Indiya, kuma sun hada da ilmin likitanci, da taurari da lissafi da  sauransu zuwa harshen larabci.

Al-domieli wani marubucin kasar italia ya bayyana cewa, ya fada a cikin wani littafinsa, yana cewa ilmin kasar Indiya yayi tasiri sosai a al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi.  

A shekara ta 154 hijira, wasu malamai daga kasar India sun zo wajen sarki mansur dawniki daya daga cikin sarakunan Abbasiyawa,  daga cikinsu akwai fitaccen malami wanda ake kira Mankeh ya kore a ilmin lissafin taurari, da falaki musamman salon Reej, wanda wani masanin kasar ta India mai suna Barhamah Gupito ta tsara.

Da farko mansur ya bukaci ya koyawa malaman musulmi ilmin taurarin da yake da shi sannan ya bukaci a tarjama littafin Barhama zuwa harshen larabaci.

Malaman tarihi sun bayyana cewa an ci gaba da karantar da ilmin sanin taurari na Minkeh a kasashen musulmi har zuwa zamanin sarki Mamoon dan sarki Haruna rasheed.  Sun ce sarki Mamoon ya umurci Ibrahim Farrazi, sanennen malamin taurari musulmi, ya rubuta masa salon ilmin taurari na kasar Indiya don amfanin malamai musulmi.

Abu raihan biruni, ya kawo a cikin littafinsa na ayyukan sa, inda yake cewa, ya samu ana karatun littafin farrazi. Haka ma likitancin kasar indiya ya sami shiga cikin al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi.

Sai kuma Ibn Nadim wanda ya kawo a cikin littafin Fehres, sunayen littafai guda 12 duk kan ilmin likitanci na kasar indiya. Wadanda aka tarjama a farkon daular Abbasiyawa. Wannan ya bawa musulmi da dama sanin tsirrai, da ma’adinai da kuma dabbobi  masu maganin cututtuka daban daban. Duk wadanda suka samu daga malaman kasar Indiya.

 Amma dangane da ilmi da kuma fahinta a zamani kafin bayyana musulunci a Iran, an kai kololuwan ilmin Iraniyawa ne a zamanin nsarki Khusru Anooshirvan. Kuma cibiyar wadan nan ilmomi garin Shapoor daga cikin garuruwan Shushtar da desful.

An kafa makarantu daban daban a wadan nan wurare, sannan an kira malamai daga cikin kiristocin siryanawa da daliban daga ko ina zuwa wadannan makarantun suna yada ilmomi daban daban.

An kawo wasu littafan da harshen siryaniyanci, wasu kuma da harshen girka duk aka tarjamasu da yaren farisanci na Pahlavi. A shapoor an tarjami ilmin likitanci zuwa harshen farisanci. Kuma wannan ya faru ne tun cikin kimanin karni na 4 miladiyya wato shekaru kimani fiye da 200 kafin bayyana musulunci.

An tarjama littafan Aroto da Aflatun ton lokacin zuwa harshen Pahlavi na farisanci. Sanna bayan shigowarn addinin musulunci kasar Farisa an tarjama wadan nan littafan zuwa harshen larabci.

Haka ma a cikin daular Abbasiwa an tarjawa wasu littafan da dama daga harshen Pahlavi zuwa larabci. A lokacin mulkin sarki Haruna Rashid, waziransa yan gidan Barmaki sun tarjama littafai da dama daga Pahlavi zuwa larabci.

A lokacin malaman Iraniyawa da dama suka je bagdaza inda suka tarjama littafan ilmi da dama daga harshen farisanci na lokaci ko Pahlavi zuwa larabci.

A lokacinda an tarjama ilmin sani ko lissafin da taurari zuwa harshen larabaci. An kira malamai da dalibai na makarancin Shapoor zuwa Bagdaza don wannan aikin.

Ibn Nadin ya kawo a cikin  littafin fehrest kan cewa malamai kuma likitoci daga yan gidan Nubakhti sun taimaka wajen tarjamar littafai daga harshen Pahlavi zuwa larabci.

Ya ce: Abu Sahal dan Noobakht malamin taurari na mansur, da kuma dansa Hassan dan Sahal suna daga cikin wadanda suka tarjama littafan ilmin taurari daga harshen farisanci na lokacin zuwa larabaci. Ya ce Abu Sahal ne ya tarjama littafin ‘Zeeje Shahriyar, zuwa harshen larabci.

An rubuta Zeeje Shahriyar ne a zamanin sarkin sasaniyawa Yazdajar na 3. A cikin wannan littafin lissafin kwanaki da yini yana dai dai da yanda yake a wannan zamanin. Kama daga tsakiyar dare da da sauran dare da rana, babu wani bambanci. Wato kamar yanda malaman girka da da sauran turawa suke lissafi har zuwa shekara 1925M, inda suke fara irgen kwanaki daga tsakiyar dare.

A farkon bayyanar addinin musulunci hankalin musulmi ya koma kan fadada daular musulunci ne don tabbatar da ita a kan kafafuwanta. Don haka bayan da suka sami haka a daulolin banu Umayya da kuma Abbasiyawa, sun suka koma kan neman ilmi da kuma kafa masana’antu.

Don haka kuma, bayan tabbatar daular musulunci tare da futuhat da aka samu, sarakunan Abbasiyawa a Bagdaza sun sami kudade masu yawa a lokacin, don haka sai suka fara kwadaitar da musulmi zuwa karatu da kuma tarjamar littafai zuwa harshen larabci, saboda mafi yawan wadan nan ilmomi suna wajen harshen laranci ne. Sai dai ilmin na farko da suka sa a gaba, shi ne ilmin Alkur’ani mai girma, koyin karatunsa yanda ya dace da kuma riko da ibadu musamman sallah wacce ake karanta Alkur’ani mai girma a cikinta. A lokacin da aka fara neman ilmimomi na kasashen waje, da kafa masana’antu musulmi suka fara samun kudade suka kuma fara wadata.

Ilmin alkur’ani mai girma ya bude kwakwalen musulmi a kan neman ilmi da kuma neman sanin al-amura. Don haka, sun bazama zuwa duk inda zasu sami ilmi. Wannan ya sa a cikin dan karamin lokaci musulmi sun kore a sana’o’ii da dama, sun kafa masana’antu sun kuma kware a dukkan ilmin da suke bukata don ci gaba, wanda babu wanda ya kaisu a duk duniya a lokacin.

Don irin yawan ci gaban da aka samu a lokacin, a duniya a kuma zamanin, ana kiran wancan zamanin a matsayin zamanin “Yunkuri ci gaban al-adu da ci gaban addinin musulunci’.

Mufi muhimmanci daga cikin al-amuran da suka taimaka wajen wannan yunkuri shi ne tarjaman ilmi zuwaharshen larabci, kamar yanda Ibn nadim ya kawo a cikin feherest. Wannan littafin ya kawo wani bangare na ilmin magabata da kuma tarihin yunkurin ci gaban musulmi a lokacin har zuwa karni na 4 bayan hijira.

Tun daga lokacin har zuwa yau, da wuya ka sami wani abu na al-adu da ci gaban musulunci wanda ibn Nadim bai kawo ko da kadan ne daga ciki ba.

Banda Fehrest na ibn dadim, sai littafi mai suna ‘Dabakat Atibbaa wa Akhbar Al-ulamaa’ wanda ibn Qifti ya rubuta. Shi ma wani littafin tarihi da al-adun musulunci ne. A cikinsa malamai masu bincike sun yi bincike sun kuma kawo al-amura da suka taimaka wajen yunkuri da kuma samar da al-adu da ci gaba a tarihin addinin musulunci da kuma dalilan da suka haddasa faduwar daular da kuma ci gaban daga baya.

A cikin zamanin banu umayya an tarjama wani littafi dangane da ilmin likitanci, sarki Marwan na farko ya bada umurnin a tarjama wannan littafin mai suna ‘Konnash’ wanda Mosurjuye ya rubuta.

Sai dai a zamanin daulolin banu umayya an fi tarjamar littafai wadanda suka shafi, al-amuran harkokin shugabanci, tsara harkokin tafiyar da gwamnati, harkokin kasuwanci da makamancisu, wannan saboda suna son sanin yanda zasu tafiyar da harkokin mulki da kuma hulda da yan kasashen waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted