Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta sanar da nasarar kai harin ramuwar gayya kan rijiyoyin mai da wuraren adana makamai a sansanin sojin sama na Amurka na Yarima Hassan a kasar Jordan a matsayin ramuwar gayya ga hare haren Amurka a wasu sassan kasar.
Ma’aikatar Hulda da Jama’a ta IRGC ta bayyana a safiyar wannan Litinin cewa rundunar sojin saman ta ta kai hari kan muhimman wurare a sansanin na Amurka, wanda ke zama cibiyar da ke da matukar muhimmanci ga sojojin Amurka.
Wannan farmakin ya haifar da gobara a wuraren ajiyar mai da wuraren adana makamai, wanda hakan ya lalata kayan aiki na Amurka da kuma tsare tsarenta a Yammacin Asiya.
Sanarwar ta ce an gudanar da aikin ne a matsayin martani kai tsaye ga harin da Amurka ta kai wa sansanin bakin teku na Iran.
Wannan matakin ya zama wani bangare na matakin farko na martanin da Iran ta tsara kan hare-haren Amurka na baya-bayan nan, ciki har da hare-haren sama kan sansanonin bakin teku na Iran da kayayyakin sadarwa a kudu.
IRGC ta jaddada cewa an kai hare-haren ne ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka.
A lokaci guda kuma Sojojin Iran sun kai hare-haren jiragen sama marasa matuki akan wasu wurare da ke da alaka da Amurka, ciki har da tsarin tsaron sararin samaniya na Patriot, rumbun makamai, da kuma wasu cibiyoyin sadarwa na radar na Amurka a Kuwait da Bahrain.
IRGC ta kuma yi gargadin cewa duk wani ci gaban ayyukan Amurka zasu fuskanci martani mai tsauri.