Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun sanar da cewa, sun kai hari akan jirgin Amurka na dakon jiragen yaki da kuma wani jirgin Ruwan na daban na yaki.
Sanarwar ta ce dakarun kare juyin musuluncin ta kuma ce sun yi amfani ne da makamai masu linzami samfurin “Ballastic” wajen kai harin da ya tilastawa jiragen yakin na Amurka ja da baya zuwa wuri mai nisa.
Dakarun na “IRGC” sun ce,sun kai wa wadannan jiragen na Amurka hari ne saboda suna takurawa jiragen Ruwan Iran da kuma shiga cikin killace Iran.
Jiragen yakin na Amurka sun gudu daga wurin da aka kai musu harin, saboda tsoron kar su sake fuskantar wani harin.
Haka nan kuma IRGC sun ce;makiya da suke kai da komowa a cikin wannan yankin cikin nuna isa da girman kai na bogi, bayan harin sun yi furuci da cewa an kai wa jiragen yakin nasu hare-hare.
Dakarun kare juyin musuluncin na Iran sun kuma jaddada cewa za su ci gaba da kare kasa ta kowace fuska,kuma yadda al’ummar kasar suke tarukan nuna goyon baya da kuma tsayin dakar sojoji za su hana abokan gaba cimma manufofinsu.
Wani sashe na bayanin dakarun kare juyin ya kunshi cewa, idan har Amurka su ka ci gaba da takurawa Iran to su tsammaci mayar da martani mai tsanani.