Kasashen duniya sun ci gaba da yin tir da HKI saboda hare haren da ta kai kan karamin ofishin jakadancin kasar Iran da ke birnin Damascus babban birnin kasar Siriya a jiya da yamma.
Kamfanin dillancin labaran ‘Iran-Pars’ ya bayyana cewa gwamnatocin kasashen Rasha, Pakistan, Omman, hadaddiyar daular Larabawa, da Qatar duk sun yi allawadai da hare haren na HKI kan karamin ofishin jakadancin JMI a kasar Siriya.
Ma;aikatar harkokin wajen Rasha ta bukaci HKI ta kawo karshen ayyukan ta’adancin da take yi a yankin kudancin Asiya. Ta kuma bukaci dukkan kasashe a MDD su bayyana matsayinsu a kan yadda HKI take take dokokin kasa da kasa a yankin.
Mumtaz Zahra kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta bayyana cewa hare haren HKI kan ofishin jakadancin JMI a Damascus ya sabawa dokokin kasa da kasa.
Janar Muhammad riza Zahidi da kuma Janar Muhammad Hadi Hajj Rahimi da wasu mutane 5 tare da su ne suka yi shahada a hare haren na HKI a birnin Damascus.