Ministan harkokin wajen JMI da kuma tokwaransa na kasar Masar sun tattauna da wayar tarho a jiya Lahadi, inda bangarorin biyu suka tabo batutuwan da suka hada da dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma matsalolin yankin wadanda suka hada da yaki a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya kara da cewa an sami nasarori da dama a cikin yan watannin da suka gabata tsakanin kasashen biyu musamman dangane da kwautata dangantaka tsakaninsu.
Har’ila yau sun tattauna batun ganawar shugaban kasar Masar Sayyid Ibrahim Ra’isi da tokwaransa na kasar Masar a birnin Jidda na kasar Saudiya a cikin watan Jenerun da ya gabata.
Dangane da yakin Gaza kuma Amir Hussain Abdullahiyan ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana damuwarsa da ci gaba da kissan kiyashin da gwamnatin HKI take yi a Gaza, da kuma gazawar kasashen duniya wajen taka mata birki.
A nashi Bangaren Sami Shukri ministan harkokin wajen kasar Masar ya bayyana cewa gwamnatin kasar ba zata amincewa HKI ta tilastawa mutanen Gaza shiga kasar Masar daga garin Rafah ba.