Afrika Ta Kudu Ta Zargi Najeriya Da Karya Kan Huldar Diflomasiya

kasar afrika ta kudu ta zargi najeriya da karya kan huldar diflomasiyar dake tsakanin kasashen guda biyu

Najeriya da Afirka ta Kudu sun sake samun sabani a huldar diflomasiyya, bayan kakakin shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya zargi babban ofishin jakadancin Najeriya da yin karya kan ikirarin cewa shugaban kasar ya sa baki bayan cire jawabin Ambasada Femi Fani-Kayode daga cikin shirye-shiryen da gidan talabijin na kasar ya watsa na wani bikin diflomasiyya.

Vincent Magwenya, kakakin Ramaphosa, ya ce shugaban kasar bai sa baki a lamarin ba, kuma kundin tsarin mulkin kasar bai ba shi ikon tsoma baki cikin shawarar editocin gidan talabijin din kasar, SABC, ba.

Rikicin ya ƙara kamari a yau Asabar, bayan babban ofishin jakadancin Najeriya ya sake jaddada matsayarsa kan abin da Fani-Kayode ya bayyana. Ofishin jakadancin ya dage cewa an wulakanta ambasadan, tare da cewa Ramaphosa da kansa ya sa baki wajen aikata wulakancin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted