Shugaban bangaren siyasa na kungiyar hizbullah ta kasar labanon ya bayyana cewa iran ta tabbatarwa da Amurka cewa akwai kasa da za ta iya tunkarar ta, kuma ta nunawa washington cewa yanzu ba itace kasa mafi karfi ba,
Sayyid Ibrahim amin ya fadi a wata hira da yayi da gidan talabijin din al-manar cewa ci gaban da aka samu a kasar iran da labanon da yamen ya canza tunanin mutane a duniya, da kuma alakar dake tsakanin kasashe da kuma gwagwarmayar da ake ci gaba da yi a matakin kasa da kasa
Yace iran ta tona asirin iyakar karfin sojin Washington da kuma karfin siyasarta a arangamar da ta yi da amurka da isra’ila, haka zalika yace trump yana kokari ganin ya tabbatar da karfin amurka a duniya amma yana fuskanta rashin nasara a hanyar da ya kama
A karon farko a tarihin amurka mun shaida zaben da aka gudanar tsakanin wadanda ke nuna adawa da kai wa kasar iran hari da kuma masu nuna goyon bayan kai mata hari , kuma a karon farko mun shaida yadda kasashen turai ke canza matsayarsu kan isra’ila