Wasu Jiragen Ruwan Dakon Mai Sun Kama Da Wuta A Hormuz

Jami’an Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci sun sanar da cewa: Jairagen ruwa masu dakon mai guda biyu sun fashe a Mashigar Ruwan Hormuz Ofishin Hulɗa

Jami’an Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci sun sanar da cewa: Jairagen ruwa masu dakon mai guda biyu sun fashe a Mashigar Ruwan Hormuz

Ofishin Hulɗa da Jama’a na Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta (IRGC) ta sanar da cewa: Jiragen ruwa biyu masu ɗauke da mai sun kama da wuta a mashigar ruwan Hormuz da ke kudancin teku.

A cikin wata sanarwa da Ofishin Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojojin Ruwa ta IRGC ya fitar ya ce: Jiragen ruwa biyu masu ɗauke da mai da ke ƙoƙarin ratsawa ta mashigar ruwan Hormuz ba bisa ƙa’ida ba sun afka ta nakiyar ruwa a mashigar ruwan teku kuma sun kama da wuta.

Sanarwar ta ƙara da cewa: Bayan fashewar, wasu jiragen ruwa biyu da suka yi ƙoƙarin ratsawa ta mashigar ruwan Hormuz sun saurari gargaɗin da Cibiyar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Ruwa ta Rundunar Sojojin Ruwa ta IRGC ta yi, suka koma kan tsarin Tekun Farisa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted