Sojojin Yamen Sun Kai Hari Kan Jirgin Sama Mara Matuki Na Saudiya

sojoji yamen sun harbo jiragen yakin leken asiri na kasar saudiya a lardin aljwf na kasar yamen

Dakarun sojin kasar yamen sun harbo wani jirgin sama mara matuki na leken asiri na kasar Saudiya a lokacin da yake kokarin kai hari a arewacin lardin al-jawf na kasar yamen

Kakakin dakarun sojin kasar yamen brigadier janar yahya saree ya sanar cewa da safiyar yau lahadi dakarun tsaron sararin samaniyar kasar yamen sun kai hari kan jirgin leken asiri mai dauke da makamai na ch-4 adaidai lokacin da take gudanar da ayyukan ta’addanci

Haka zalika kakakin sojin na yamen yace an harba makamai masu linzami guda biyu a kan cincirindon sojojin kasar saudiya a yankin al-tuwal  dake kudu maso yammacin Jazan, inda ya kashe sojoji da dama da kuma jikkata adadi mai yawa, kuma dakarun sojin kasar Sudan dake goyon bayan saudiya na daga cikin wadanda abin ya shafa.

Yakin da kasar saudiya ta kaddamar kan kasar yamen yayi sanadiyar mutuwar dubban daruruwan mutanen yamen. amma duk da haka bata iya cimma manufarta ba akan kasar na kafa gwamnati da za ta zama yar korenta ba

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted