Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Amurka ta wofantar da diflomasiyya da tattaunawa duk da muhimmancin da ke cikinsu
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i, yayin da yake magana kan rahoton da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya ta fitar na kwata na baya-bayan nan game da Iran, ya yi ikirarin cewa: Shirya rahotanni na gefe ɗaya kan shirin makamashin nukiliyar Iran ya lalata amincin hukumar a matsayinta na hukuma ta ƙasa da ƙasa mai iko kan al’amuran makamashin nukiliya.
Da yake amsa tambaya game da ikirarin da Babban Sakataren Majalisar Haɗin Kan Kasashen yankin Tekun Farisa ya yi a lokacin zaman Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya ɗora wa Iran alhakin hare-haren da aka kai wa wasu ƙasashe a yankin, sannan ya buƙaci Iran ta biya diyya, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya ce: “Kada ku ɗauki wannan ikirarin da muhimmanci; su da kansu sun san cewa waɗannan zarge-zargen ba su da tushe.”
Dangane da shawarwarin da Iran ke yi da China da Rasha, Baqa’i ya bayyana cewa: Ana ci gaba da tattaunawa da China da Rasha kuma ana gudanar da su ta hanyar kiran waya da tarurruka kai tsaye. Ya ƙara da cewa: Iran tana ci gaba da tuntuɓar ofisoshin jakadancin China da Rasha a Tehran.