Ofishin Jakadancin Iran A Afirka Ta Kudu Ya Yi Ba’a Wa Amurka

Ofishin jakadancin Iran ya yi wa jami’an Amurka ba’a cewa: Idan ku yi nasara a yaki da Iran to, ku fito daga maboyanku! Ofishin Jakadancin

Ofishin jakadancin Iran ya yi wa jami’an Amurka ba’a cewa: Idan ku yi nasara a yaki da Iran to, ku fito daga maboyanku!

Ofishin Jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke Afirka ta Kudu ya mayar da martani ga Sakataren Baitulmalin Amurka Scott Bisent da ya buya a sansanin soja saboda tsoron Iran, da kuma kalaman batanci da ya yi kwanan nan kan Iran, yana mai cewa: Wadanda ke ikirarin yin nasara ya kamata su fito daga wuraren da suka ɓuya su bayyana kansu.

Ofishin Jakadancin Iran ya buga wani sako a dandalin X, yana ikrarin cewa: ‘Yan Iran, tare da tsohon wayewarsu da kuma al’adun jarumtaka da girmamawa, ba su da wata alaƙa da ta’addanci ko tsoro.

Sakon ya ci gaba da cewa: “Marco Rubio, Scott Bisent, Pete Higseth da sauran jami’an Amurka wadanda ke rayuwa cikin tsoro koyaushe, suna cikin mafarkai na laifuffukan da suka aikata, kuma wadanda yanzu ke neman mafaka a matsugunan sojoji don kare su, za su iya nuna fuskokinsu ga jama’a lokaci zuwa lokaci.”

Ofishin Jakadancin na Iran ya kara da cewa, a cikin wata magana mai ban dariya ga kalaman da jami’an Amurka suka maimaita game da nasara a yakin da suka yi da Iran: “Sanarwar nasara, al’ada da suke maimaitawa duk mako har sai ta zama shirin talabijin mara iyaka, yana buƙatar wani ya isar da wannan sakon ga mutane.” Saboda haka, ya fi kyau ga waɗanda ke da’awar cewa sun sami nasara su fito daga maɓoyarsu su bayyana nasarar da kansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted