Sojojin Isra’ila Sun Kashe Samir Abu Yunus Babban Kwamanda

sojojin isra'ila sun kashe babban kwamandan kungiyar izzud deen qassam samir abu yunus

Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta tabbatar da shahadar Samir Mahmoud abu yunus da ake fi sani da abu mahamoud  kwamanda a kungiyar Izzudden Qassam bangaren soji na kungiyar Hamas a wani hari da sojojin isra’ila suka kai masa a yankin falasdinu

Kungiyar Qassam ta bayyana cewa abu mahamoud yana daga cikin yan gwagwarmaya na farko- farko da ya hade da bangaren soji na kungiyar tun a shekara ta 1991, ya zauna na tsawon lokaci a gidan yarin isra’ila, kuma shi ne ke jagorantar wasu hare -hare da dama da ake kai wa isra’ila

Haka zalika ta kara da cewa Abu mahamoud yana daga cikin fitttun kwamandoji dake da hannu wajen shiryawa da kuma kaddamar da harin ambaliyar Aqsa mai cike da tarihi da aka kai wa isra’ila hari a ranar 7 ga watan oktoban shekara ta 2023

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted