Rahotanni sun bayyana cewa dakarun kare juyin musulunci na iran sun bayyana cewa sun kai hari kan na’urorin radar tsaron sararin samaniyar a sansanin sojin Amurka dake kasar Bahrain da jiragen sama marasa matuki guda 6.
Ta fitar da wannan bayanin ne a yau lahadi, inda ta bayyana cewa jiragen sama marasa matuki sun kai hari kan radar tsaro, a mataki na biyu na mayar da martani kan hare haren da kasar Amurka ta kai kan kasar iran, kuma an samu nasara sosai a harin da ta kai a sansaninta na Bahrain
Haka zalika dakarun na IRGC ta gargadi Amurka game da kokarin da take yi na karkatar da hankulan duniya kan batun da ya shafi mashigar Hormuz, na daukar mataken rashin da’a. sakamakon rashin nasarar da ta samu na matakin da take dauka na yin rakiya ga jiragen ruwa ta yin fasa kwabrin wucewa ta mashigar hormuz
Idan ana iya tunawa tuni jami’an kasar iran suka yi gargadin cewa duk wani hari da Amurka za ta kara kai wa iran to zai hadu da mayar da martanin nan take ba tare da la’akari da iyakar taswirar kasa ba, musamman wajen kare mashigar hormuz