Wata kotu a Jordan ta yanke hukuncin kisa kan mutane uku da aka samu da laifin kai harin cocin Karak, yayin da aka yanke wa wasu biyu hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari
Kotun Tsaron Kasa a kasar Jordan ta yanke wa mutane uku hukuncin kisa a safiyar Lahadi saboda kai hari da makami a Cocin Orthodox na Girka na St. George da ke Hammoud, a gundumar Karak, kudancin Jordan, a ranar 23 ga Oktoba, wanda ya yi sanadiyyan mutuwan mutane tara. Kotun ta kuma yanke wa wadanda ake tuhuma na hudu da na biyar hukuncin daurin shekaru shida kowannensu a gidan kurkuku.
Hukuncin ya zo ne bayan da kotun ta samu wadanda suka aikata laifukan su uku da laifin aikata laifuka da dama da aka tanada a cikin Dokar Yaki da Ta’addanci ta Jordan, musamman aikata ayyukan ta’addanci da suka kai ga mutuwa, da kuma aikata ayyukan ta’addanci ta hanyar amfani da makamai da harsasai.
Laifukan da kotun ta yanke wa masu laifin sun haɗa da mallakar makamai da harsasai da nufin amfani da su a ayyukan ta’addanci, makircin aikata ayyukan ta’addanci ta hanyar amfani da makamai, da kuma tallata ra’ayoyin wata ƙungiyar ‘yan ta’adda.