Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kanaan ya fadi cewa iran tana taka muhimmiya rawa tare da yin aiki tare da sauran kasashen duniya wajen samar da zaman lafiya da sulhu a yankin gabas ta tsakiya da yaki da ta’addanci da ma kasa da kasa,
Haka zalika kakakin ya tir da matakin da wasu kasashe 3 Amurka Birtaniya dad a kuma kasar Kanada na kakaba takunkumi kan wasu jami’an sharia da wasu manyan jami’an soji na kasar Iran , da kuma kudurin da majalisar tarayyar turai ta fitar kan kasar iran,
Daga karshe ya bayyana cewa alumma da gwamnatin iran sun dauki takunkumin da kasashen turai ke sanyawa Iran a matsayin wata dama ta dogaro da kanta wajen ci gaba da kara shiryawa a bangaren tsaro da kuma soji.