Shugabann kasar Iran mas’ud pezeshkiya yayi kira ga mambobin kungiyar tattalin arziki ta Bricks da ta gina hanyoyin kasuwanci mai karfi kuma ta fadada hanyoyin amfanin da kudaden ta na cikin gida don karfafa karfin tattalin arziki, da yin aiki tare domin rage dogaro da wasu da kuma matsalolin siyasa
Shugaban yana Magana ne a wajen taron cinikaiyya na shuwagabannin kungiyar Bricks da ake yi a birnin new delhi na kasar Indiya a yau jumaa , kuma yace yau duniya tana kan wani gwadabe mai cike da rudani, yana ishara game da rashin tabbas na siyasar kasa da kasa dake kawo cikas ga tsarin samar da kayayyaki da kuma karuwar amfani da mataken tattalin arziki wajen yin matsin lamba na siyasa
Ita dai kungiyar bircks asalinta ta kunshi kasashen Brazil, rasha, indiya, china da kuma kasar Afrika ta kudu, kafin daga bisani a fadada ta a shekara ta 2024 inda aka shigar da kasashen masar, Ethiopia, iran, hadaddiyar daular larabawa,, Saudi arebiya sai kuma indonesiya ta shiga a shekara ta 2025 sai kuma kasashen Balarus, Bolivia, Kazakhstan ,kuba, malesiya, Nigeria ,Thailand, Uganda, uzbakistan, da vietanam kuma suka zamo mambobi a shekarun baya bayan nan
Taron koli karo na 18 na shuwagabannin kungiyar Bricks zaa yi shi ne a ranar 12 da 13 na watan satumba a babban birnin kasar indiya karkashin taken gina tushen juriya, kirkire-kirkire hadin guiwa da kuma dorewa