Kakakin sojin kasar Yamen Birgediya Janar Yahya Saree ya bayyana cewa dakarun sojin kasar Yamen sun karbe ikon kula da yanki mai fadin daruruwan kilo mita a kasar a wuri mai matukar muhimmaci dake yammacin lardin Hudaida da Ta’aiz, kuma suna kara samun ci gaba wajen kara kusantar mashigar babulmandab a matsayin wani babban koma baya ga sojojin haya da kasar Saudiya ke marawa baya
Yahya Saree ya sanar a gidan talabijin din kasar ta yamen a yau jumaa cewa dakarun sojin kasar da sauran kungiyoyin hadin guiwa za su kori sojojin haya da kasar Saudiya ke goyon baya daga yankuna guda 6 na kasar kuma sun kawar da yan bindiga daga fili mai fadin kilo mita 5400
Haka zalika Saree ya kara da cewa dakarun sojin yaman da kungiyoyin hadin guiwa sun yi nasarar kwace sansanonin sojojin haya dake samun goyon bayan kasar sudiya da su ka hada da birged 38 kuma sun kashe tare da raunata daruruwan sojoji da dama dake wajen
haka zalika kakakin yayi kira ga mayaka daga kabilu daban daban da su bada goyon bayansu ga dakarun sojin kasar Yamen domin kawar da sojojin haya yan ta’adda da kasar saudiya ke goyon baya, domin kwato yancin kasar a matsayin kasa mai cin yancin kanta.