Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya mayar da martani ga karyar da Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya yi game da Yemen da Saudiyya
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya ce: ƙaryar da Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya yi game da tsoma bakin Iran a Yemen da Saudiyya ba za ta iya maye gurbin gaskiya ba.
Isma’il Baqa’i, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya rubuta a dandalin X don mayar da martani ga zarge-zargen karya na Sakataren Harkokin Wajen Amurka game da tsoma bakin Iran a cikin batun Yemen: Ya jaddada cewa: Karyar Marco Rubio ba za ta iya maye gurbin gaskiya ba. Ansarullah kungiya ce mai zaman kanta, bata karbar umarni daga kowane bangare; kuma ba ta wakiltar wani bangare.
Baqa’i ya kara da cewa: Dole ne a bankado tushen rashin zaman lafiya a yankin a cikin tsoma bakin sojojin Amurka da manufofin mulkin mallakarsu. Da a ce Amurka ta kuduri aniyar samar da zaman lafiya da gaske, da ta dauki mataki daya mai sauki: dakatar da munanan manufofinta da kuma ayyukanta na haifar da rashin kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.