Falasdinawa Sun Yi Shahada Sakamakon Hare-Haren Isra’ila

Falasdinawa da dama sun yi shahada ciki har da yara biyu sakamakon hare-haren sojojin mamayar Isra’ila kan arewa da kudancin zirin Gaza Majiyoyin lafiya a

Falasdinawa da dama sun yi shahada ciki har da yara biyu sakamakon hare-haren sojojin mamayar Isra’ila kan arewa da kudancin zirin Gaza

Majiyoyin lafiya a yankin Gaza sun ruwaito cewa: Falasdinawa tara, ciki har da mutane hudu ‘yan gida ɗaya, sun yi shahada sakamakon hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan yankin tun daga wayewar gari a ranar Alhamis.

Majiyoyi a Asibitin Al-Shifa sun bayyana cewa: Sun karɓi gawarwakin mutane huɗu na iyalan Ahmed bayan an gano su gunduwa-gunduwa bayan wani harin bam na sojojin mamayar Isra’ila wanda suka kai kan wani gida a yankin Beit Lahiya a arewacin yankin Gaza. Sun lura cewa biyu daga cikin waɗanda abin ya shafa ‘yan mata ne masu shekaru 8 da 12.

A halin yanzu, Nasser Medical Complex ya ba da rahoton isowar wani mutum da kuma wasu mutane da dama da suka samu raunuka bayan wani harin sama da jiragen saman sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wata mota a arewacin Khan Younis a kudancin yankin Gaza.

Hukumar Tsaron Farar Hula ta Gaza ta ruwaito cewa: Falasdinawa uku sun yi shahada a wani harin jirgin sama mara matuki ciki mallakin sojojin mamayar Isra’ila a yankin Khan Younis da ke kudancin yankin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted