Wani jami’in gwamnatin Trump ya yi ikrarin cewa: Harin Iran ya lalata jiragen yakin Amurka a kasar Jordan
Wani jami’in gwamnatin Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa: Hare-haren da Iran ta kai kan sojojin Amurka sun lalata jiragen saman Amurka da dama a wannan makon a sansanin sojin sama na Muwaffaq Salti da ke Jordan.
Jami’in, wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya bayyana cewa: Harin na Iran ya lalata wani jirgin yaki na A-10 Thunderbolt II Warthog, wanda ya yi sanadiyyar rasa daya daga cikin fikafikansa, yayin da kimanin jiragen yaki na F-15 guda takwas suka lalace kuma wasu daga cikinsu an gyara su kuma sun koma bakin aiki.
Harin ya tilasta wa sojojin Amurka harba makamai masu linzami na Patriot guda 30 don dakile makamai masu linzami na Iran, a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa game da tarin makamai masu linzami na Amurka da sauran makamai masu linzami, a cewar Reuters.
Wannan ya zo ne bayan da sojojin Amurka suka samu rauni mai yawa tun kafin harin Iran na ranar Talata, ciki har da lalata jiragen sama marasa matuka ciki sama da 20, lalata jiragen yaki.