Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku kissoshin Alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
///.. Masu sauraro barkammu da warhaka, idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan(a) dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, mun tsaya inda muka yi magana dangane da yanda Umur dan Abdul Aziz sarki daga sarakunan Banu Umayya ya kawo karshen La’antar Amirul muminina (a) kan mimbarorin musulmi fiye da 70,000 a shekara ta 99 bayan hijira a lokacinda ya yau kan kujerar Khalifancin musulmi.
Ya kuma maye wuraren zagi da la’ana a cikin hudubar da wasu ayoyin al-kur’ani masi girma. Sannan shi da kansa ya bada dalilan da suka say a dauki wannan matakin na kawo karshen la’anar. Ko kuma muce mummunan bidi’ar kakansa Mu’awiya shekaru fiye da 60 bayan hijira.
Ya ce, malamin alkur’aninsa ne ya fara hana shi tare da fada masa aliyu ya je yakain Badar, kuma shine ma badar, kuma All..ya yarda da wadanda suka je Badar, kuma bai sake yin fushi da su ba tun lokacin inji shi. Sannan ya ga yanda bakin babansa Abdulazizi yake rawa idan ya zo kan la’ana a Khudubarsa, da ya tambaye shi sai ya ce masa da mutane sun san matsayin wannan mutum da ba zasu iya mulkansu ba.
Yanzun kuma sai wadanda suka yi inkarin La’antar Imam Ali(a) wanda Mu’awiya ya sunnata daga cikin sahabban manzon All..(s) da wadanda suka zo bayansu.
01-Sa’ada dan Abi wakkas. Sa’adu dan Abiwakkas daya daga cikin manya manyan sahabban manzon All..(s), baya jin dadi idan yaji Mu’awiya ko wani daga cikin ma’aikatansa suna zagin Amirulmuminina (a) a kan mimbarorin Musulmi, ba tare da yayi inkari ba, wannan duk da cewa, ya ki yayiwa Imam Ali (a) bai’a a lokacinda aka yi masa bai’a bayan kissan Khalifa Uthman.
Malaman tarihi sun bayyana cewa wata shekara bayan shekarar sulhu Mu’awiya ya je baitullahi Alharam, bayan ya kammala dawafi sai ya je darunnadwa, wato wurin taron shuwagabannin Quraishawa a jahiliyya, ya je ya kafa fadarsa a can. Daga nan sai ya fara zagin Amirulmuminina Aliyun dan Abitalib (a). Sai Sa’adu dan Abi wakkas wanda yake wurin ya yi fushi, sai ya fadawa Mu’awiya cewa:
‘Ya Mu’awiya ka ajiye ni a kan gadon sarautanka sannan ka fara zagin Aliyu ? Na rantse da All..da in sami martaba guda daga cikin martabobin da Ali yake da su ya fi mani in mallaki duk abinda rana ta fada a kansu , wallahi in kasance surukin manzon All..(s) sannan in sami abinda Aliyu ya samu na yaya daga wajenta yafi mani abinda rana da haskaka. Wallah manzon All..(s) ya fada mani abinda ya fadawa Aliyu a ranar Khaibara wato {Gobe! lalle zan bawa wani mutum tuta Yana son All..da manzonsa sannan All..da manzonsa suna son shi, bai zai kasance mai gudu (daga makiya ba), kuma All..zai mana budi ta hannunsa} wannan ya fiye mani da abinda rana ta haskaka.
Na rantse da All..manzon All..(s) ya fada mani abinda ya fada masa a yakin Tabuk: Wato
{Shin baka amince matsayinka da ni kamar yanda Haruna ya kasance da Musa ba? Sai dai babu annabi a bayana ?} Wannan yafi soyuwa a gareni daga duk abinda rana ta haskakashi.
Na rantse da All..ba zan sake shiga wani gidan da kake ciki ba , har zuwa karshen rayuwa ta, sai Sa’adu ya tashi ya barshi a fusace.