Iran: Dole Ne A Mutunta Yemen A Kawo Karshen Killaceta

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bada sanarwan cewa dole ne a mutunta yencin kasar yemen a cikin rigingimun da suke faruwa a halin yanzu

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bada sanarwan cewa dole ne a mutunta yencin kasar yemen a cikin rigingimun da suke faruwa a halin yanzu tsakaninta da kasar Saudia.

Ma’aikatar harkokin wajen ya bayyana haka ne a yau Jumma’a a wani bayanin da ta fitar. Ta kuma kara da cewa mutanen kasar Yemen mutanen wadanda suke da tarihi ciki da daukaka da kuma ilmi. Don haka mutuntasu yana da matukar muhimmanci musamman a halin da muke ciki a yankin yammacin Asia.

Labarin y ace, ma’aikatar ta bukaci a kawo karshen killacewar da aka yiwa kasar na tsawon shekaru 12 dasuka gabata, a kuma koma kan teburin tattaunawa da ita dangane da matsalolin da kasashen biyu suke sabani a tsakaninsu.

A cikin yan makonnin da suka gabatawa mayakan gwamnatin San’aa sun sami nasarori masu yawa a kan inda ta dawo da ikon gwamnatin kasar kan yankunan Hays da Al-Khawkhah da kuma garin bakin ruwa na Yakhtul sannan sun kuma kama hanya zuwa garin Mokha mai tashar jiragen ruwa a bakin tekun red Sea.

A wani bangare kuma gwamnatin kasar ta Yemen ta bada labarin hare hare ta sama na jiragen yakin kasar Saudia a wurare dadama . Labarin ya kara da cewa saudia ta kai hare hare har guda 64 a kan wurare daban daban a cikin sa’o;’ii 24 da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted