Shugaban Majalisar Dokokin Iran ya jaddada cewa: Shige-shigen kuɗi da ƙaryar Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ba su da wani tasiri kan rage farashin mai
Shugaban Tawagar Tattaunawar Iran kuma shugaban Majalisar Dokokin kasar Muhammad Baqir Qalibaf ya ce: Shiga tsakani na kuɗi da ƙarairayin Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ba su da wani tasiri wajen rage farashin mai.
Muhammad Baqir Qalibaf ya rubuta cewa: Dangane da farashin man ganga daya da ya wuce dala 105, da kuma buga wata sanarwa a hukumance da ke nuna rashin ingancin ayyukan Ma’aikatar Baitulmalin Amurka wajen rage farashi da hauhawar farashin mai a nan gaba,
A cikin wani rubutu a kan kafar sadarwa ta X: Qalibaf ya bayyana cewa: “Idan kuna neman dalilin makomar kasuwar man fetur—alhali jami’an tattalin arziki na gwamnatin Amurka sun yi shiru—bari mu duba abin da ke tafe: Ma’aikatar Baitulmali za ta kwashe dukkan dabarunta marasa tasiri na sarrafa farashin man fetur (kamar yayata labarai ta hanyar kafar Axios, shiga tsakani a kasuwa, fitar da man da aka ajiye a matsayin tanadi, da sauransu), amma bai yi wani tasiri ba wajen rage farashi. Duba wannan jadawalin, amma ku yi kamar ba ku san matakin da zai biyo baya ba.”