Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sakesaduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau. Shirin wanda yake kawo maku labarai a wannan makon da muke ciki wadanda suka shafi siyasa tattalinn arziki zamantakewa tsaro da sauransu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.
////… Madallal, masu sauraro zamu fara shirimmu na yau dalabarinm mai cewa, Iran: Dole Ne A Mutunta Yencin Kasar Yemen A Kawo Karshen Killaceta
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bada sanarwan cewa dole ne a mutunta yencin kasar yemen a cikin rigingimun da suke faruwa a halin yanzu tsakaninta da kasar Saudia.
Ma’aikatar harkokin wajen ya bayyana haka ne a yau Jumma’a a wani bayanin da ta fitar. Ta kuma kara da cewa mutanen kasar Yemen mutanen wadanda suke da tarihi ciki da daukaka da kuma ilmi. Don haka mutuntasu yana da matukar muhimmanci musamman a halin da muke ciki a yankin yammacin Asia.
Labarin y ace, ma’aikatar ta bukaci a kawo karshen killacewar da aka yiwa kasar na tsawon shekaru 12 dasuka gabata, a kuma koma kan teburin tattaunawa da ita dangane da matsalolin da kasashen biyu suke sabani a tsakaninsu.
A cikin yan makonnin da suka gabatawa mayakan gwamnatin San’aa sun sami nasarori masu yawa a kan inda ta dawo da ikon gwamnatin kasar kan yankunan Hays da Al-Khawkhah da kuma garin bakin ruwa na Yakhtul sannan sun kuma kama hanya zuwa garin Mokha mai tashar jiragen ruwa a bakin tekun red Sea.
A wani bangare kuma gwamnatin kasar ta Yemen ta bada labarin hare hare ta sama na jiragen yakin kasar Saudia a wurare dadama . Labarin ya kara da cewa saudia ta kai hare hare har guda 64 a kan wurare daban daban a cikin sa’o;’ii 24 da suka gabata.
Iran Ta Fatattaki Amurka A Sansanin Sojojin Amurka Da Ke Bahrai
Sakatarin riko na rundunar Sojojin Amurka Hung Cao ya tabbatar da cewa sojojin Iran sun wargaza sansanin sojojin ruwa mafi girma a na Amurka a yammacin Asia da ke Bahrain.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Cao na fadar haka a lokacinda yake hira ta musamman da ‘ The Epoch Times’ wanda ya gabatar da rahoton a jiya Alhamis.
Ya kuma kara da cewa, wannan shi ne rahoto a karon farko na wani babban jami’in sojan Amurka dangane da yawan asarorin da Amurka ta yi a sansanin sojojinta mafi girma a yammacin Asia bayan fara yaki da Iran a ranar 28 ga watan Fabrayrun da ya gabata.
Tashar talabijan ta FOX NEWS ta bayyana cewa kafin haka kafafen yada labarai da dama sun bada labarin mummunan halin da sojojin Amurka suke ciki a yammacin Asia, musamma a sansanin sojoji na 5Th na sojojin ruwa da suke Bahrain.
Amma wannan shi ne karon farko wannan babban jami’in sojon Amurka ya tabbatar da dukkan rahotannin da aka bayar kan wannan asarar.
Cao ya kammala da cewa, lalata sansanin sojojin Amurka na sojojin Ruwa a Bahrain ya sa kataparen jirgin ruwa mai daukar jiragen yaki wato Abraham Lincon ya kasa samun inda zai tsaya don gudanar da ayyukansa.
An Bada Labaran Gobara A Kan Butunun Man Gabas Da Yamma Na Saudia
Wasu kafafen yada labarai sun bada labarin hango hayaki mai yawa a kan bututun man wanda yake daukar danyen man fetur daga gabas zuwa yamma na kasar Saudia, wanda mai yuwa an kai masa hari ne.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya bayyana cewa wasu majiyoyi wadanda ba na hukuma ba sun bayyana cewa hare haren da aka kaiwa bututun man sun auku ne a bangarensa da ke kusa da Madina wanda kuma yake daukan mai zuwa tashar jiragen ruwa na yanbu kan bakin tekun Red sea.
Wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa akwai sojoji masu bada shawara na Amurka kima ni 100 a cikin saudia.
Wasu masana sun bayyana cewa wata ta tashi a kan bututun ne bayan takurawa wanda ya haddasa wutar. Bututun man Gabas zuwa yama dai dama shi ne kadai ya ragewa Saudia bayan rufe mashigar ruwa ta hurmuz wanda JMI ta yi a farkon wannan shekara.
HKI Ta Kai Hare Hare Maso Muni Kan Wasu Yankuna A Kudancin Kasar Lebanon
HKI ta ci gaba da kai hare hare mafi muni masu tsanani a kudancin kasar Lebanon a jiya Alhamis.
Tashar talabijan ta Al-Manar ta kasar Lebanon ta bada labarin cewa, jiragen yakin HKI sun kai hare hare kan tuddan Al- Tahir da Khiam, Mansuriyya da kuma da kuma Bani Hayyan.
Har’ila yau jiragen yakin yahudawan sun kai hare hare kan fadamar mansuri da kumaZabqin.
Kafin haka dai sojojin yahudawan sun rusa gidaje da dama a kudancin kasar ta Lebanin a cikin yan makonni da suka gabata wadanda kuma suka kashe daruruwan mutane.
A dayan bangaren kuma gwamnatin kasar Lebanon wacce ta dage kan tattaunawa da HKI al-hali tane ci gaba da mamayar kasar Lebanon, ta fara fahintar cewa tattaunawa da yahudawan ba inda zai kaita sai kara rasa kasar Lebanon da kuma rayukan mutanen kasar, saboda sojojin yahudawan ba zasu taba janyewa daga kasar ba sai da karfi. Da kuma gwagwarmaya.
IRGC Ta Lalata Wani Jirgin Ruwan Leken Asirin Amurka A Hurmuz
Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun bada labarin gano da kuma lalata wani jirgin leken asirin Amurka wanda ake sarrafashi daga nesa a bakin mashigar ruwa ta Hurmuz a jiya Alhamis da yamma.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar IRGC reshen ruwa wato Navy na fadar haka a bayaninta na 16.
Bayanin ya bayyana cewa a cikin yan kwanakin da suka gabata sojojin Amurka sun kasa zuwa da sojojinsu a bakin tekun farisa saboda tsoro don haka ne suke amfani da jiragen ruwa wadanda ake sarrafasu daga nesa, don ayyukan leken Asiri.
Labarin ya ce wannan karon sun aiko sun aiko da wani jirgin ruwa kan doron ruwa, wanda ake sarrafashi daga nesa saboda ayyukan leken asiri. Mai lamba 5838, jirgin ya isa bakin mashigar ruwa ta Hurmuz a lokacinda sojojin ruwa na dakarun suka gano shi suka kuma lalata shi.
Bayan haka dakarun sun bada sanarwan cewa an rufe mashigar ruwa ta Hurmuz har zuwa abinda hali yayi. ============.
Anasarallah Na Kasar Yemen Sun Kakkabo Dron Na Uku Daga Kasar Saudia
Kakakin sojojin kasar Yemen ya bada sanarwan kakkabo jirgin Drone na kasar Saudia karo na 3 a cikin sa’ai 24 da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto burgedia Yahyah Saree yana fadar haka a jiya litinin kan cewa sojojin kasar sun kakkabo makamin Drone samfurin Wing Loong II a dai dai lokacinda yake kai hare hare a lardin Al-Baida.
Saree ya kara da cewa wannan shi ne makamin Drone na kasar Saudia da muka kakkabo a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata.
Gwamnatin kasar Yemen ta San’a ta bada sanarwan killace jiragen ruwan dakon main a kasar Saudia a watan Yulin da ya gabata, har zuwa lokacinda zata dauke mata takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata na tsawon shekaru 12 da suka gabata.
Kafin haka a shekara ta 2015 kasar Saudia da kawayenta suka farwa kasar Yemen da yaki da sunan maida Abdurabbu Mansur hadi kan kujerar shugabancin kasar, amma bayan fafatawan da babu nasara na shekaru 8 an tsagaita wuta, ammam kuma ta ci gaba da dorawa kasar takunkuman tattalin arziki ta sama da kasa da ruwa.
Iran: Muna Sanya Ido Sosai A Kan Iyakokin Kasar
Babban kwamandan sojojin kasa na JMI ya bayyana cewa sojojinsa suna sanya ido a kan iyakokin kasar dare da rana, kuma ba zasu bar wani motsi ko menene karancinsa daga wajen matsakiya su karato kan iyakokin kasar ba.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Ali Jahanshahi yana fadar haka a garin Zanjan.
Labarin ya kara da cewa Janar Jahanshahi ya bayyana haka ne a lokacinda yake ganawa da gwamnan lardin Zanjan, ya kuma kara da cewa, shojojinsa a shirye suke su tabbatar tsaron kan iyakokin na kasar Iran dare da rana ba tare da ghafala ko kadan ba.
Janar Jahanshahi ya kara da cewa aikin sojojin kasa a wannan lokacin mai hatsari wanda JMI ta shiga yana da muhimmanci. Don haka babu sako sako da aikin sojojin kasa na tabbatar da tsaro a ciki da kan iyakoki JMI.
A cikin ziyarar da babban kwamandan jojin kasan ya kai Zanjan ya ziyarci runduna ta 216 na shahid Gholamreza Mukhbiri Zanjan don ganewa idanunsa yanda suke tafiyar da aikinsu.
Araqchi: Komawar Amurka Kan Takardan Fahuntar Juna Ta Islamabd Shi Ne Matakin Farko…
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa komarwa Amurka kan takardan fahintar juna ta Islamabad shi ne matakin farko na sake dawo da zaman lafiya a yankin yammacin Asia.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya nakalto Aragchi yana fadar haka, a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa ta kasar Japan Toshimitsu Motegi a yau talata.
Labarin ya kara da cewa ministocin biyu sun tattauna al-amura da suka shafi kasashen biyu da kuma na yankin da kuma na kasa da kasa. Aragchi ya danganta halin da ake ciki a yankin yammacin Asia da abinda Amurka tayi na ficewa daga yarjeniyar fahintar juna ta Islamabad bayan yakin kwanaki 40 ko yakin Ramadan.
Ministan ta kammala da cewa, idan ana son kawo karshen halin da ake ciki a yankin, to kuwa dole ne Amurka ta koma kan MOU na Islamabat, kuma shi ne matakin na farko na rage tashe tashen hankula da suke faruwa a yankin.
Burtaniya Ta Fadada Takunkuman Bangare Guda Kan Kasar Iran Gwamnatin kasar Burtania ta kara fadada takunkuman tattalin arziki na bangare guda wanda dama ta dade da dorawa JMI.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya ce, kamar yanda aka santa da nuna tsananin adawa da JMI gwamnatin kasar Burtania a wannan karon ma ta fadada takunkuman da ta dorawa kasar wadanda suka hada da kudade, harkokin kasuwanci da kuma zirga zirgan jiragen sama.
Labarin ya kara da cewa, a wannan karon Burtania ta fadada takunkuman tattalin arziki wanda ya hada da jiragen ruwan, sannan ta kara tsuke hanyar mu’amala ta kudade da tsarin kudade na kasar Burtania, a bangaren kasuwanci kuma ta kara rege yawan kayakin kasuwanci tsakanin kasashen biyu, kuma a halin yanzu sun hada har da ilmin kimiya lissafi na kayakin lantarki, da kuma dukkan ayyukan gyaran jiragen sama da sauran injuna.
A bangaren zirga zirgan Jiragen sama kuma Burtania ta haramtawa jiragen saman Iran sauka a kasar Burtania sai tare da izini na musamman.
A lokacinda yake kokarin dalilin daukar wannan matakan na nuna adawa da JMI sakataren ma’aikatan harkokin wajen kasar burtania Stephen Doughty ya ce sun yi haka ne don hana Iran mallakar makaman Nukliya.