Iran Ta yi Gargadi Game Da Amfani Da IAEA Ta Hanyar Siyasa

kasar iran tayi gargadi game da amfani da hukumar IAEA ta hanyar siyasa don kare matakin yaki da dauka akanta

Rahotanni sun bayyana cewa Iran ta yi gargadi game da kokarin siyasantar da hanyoyin yin amfani da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, ta ce ana zargin darakta janar  din hukumar da raunana matsayin hukumar da kuma yancinta , da kuma kokarin mayar da rahotonnin fasaha zuwa hujjar siyasa don tabbatar da hare haren soji da aka kai mata

A cikin bayanin da ya wallafa  shafinsa na X kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baqa’I yace hukumar makamshin nukuliya ta duniya ta dogra ne kan kwarewa kan fasaha  da rashin nuna banbanci da kuma cin gashin kai , yace sai dai daraktan hukumar ya koma kamar wani sashi na hada rahotannin fasaha da hujjojin siyasa da  kuma hada hujjojin da suka shafi yaki

Kakakin yayi gargadin cewa lamarin ya wuce batun lalata sunan hukumar kula da makamashin nukiliya ta majalisar dinkin duniya ko na babban darakattan hukumar , yace an tozarta babban abin da yake da muhimmancin ga hukumar wato aminci da ake da shi da ita a matsayinta na hukuma mai zaman kanta kuma mai adalci ga kowa

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted