Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi tir da HKI dangane da hare haren da ta kai a baya bayan nan zuwa kudancin kasar Lebanin, inda suka kashe mutanen yankin da dama suka kuma jikata wasu.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Esma’il baghaei yana fadar haka a safiyar yau Talata ya kuma kara da cewa hare haren har’ila yau sun lalata gine gine da wurare masu muhimmanci a yankin ya kuma lalata gidajen mutane da dama.
Baghaei ya bayyana cewa sojojin yahudawan sun aikata irin wadanan hare hare a jare cikin kwanakin da suka gabata.
Ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa kama daga MDD da kuma kwamitinb tsaro na majalisar su yi magana a kan irin wadan nan ta’asan da yahudawan suke aikatawa, yace shirun da suka yi shi yahudawan suke samun kwarin guiwar ci gaba da aikata abinda suka ga dama a yankin.
Daga karshe Baghaei ya bayyana cewa, Amurka, a matsayinta na kasa tilo wacce take goyon bayan HKI a kan duk wadan nan ta’asan da take aikatawa itama tana da laifi ko kuma hannu a cikin mummunan ayyukanta.
Daga karshe kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yabawa kungiyar hizbullah wacce ta tsaya daram don kare kasarsu daga mamaya, suke kuma kare mutunci da diyaucin kasarsu da rayukansu da kuma dukiyoyinsu.