Iran ta sha Alwashin maida Martani mai karfi ga duk wata sabuwar barazana

Majalisar Tsaron Ƙasa Ta Yi Allah wadai da karuwar barazanar baka da kuma maganganun da ba su dace ba da kiyaya musamman daga Amurka da

Majalisar Tsaron Ƙasa Ta Yi Allah wadai da karuwar barazanar baka da kuma maganganun da ba su dace ba da kiyaya musamman daga Amurka da ake wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Majalisar ta yi gargaɗin cewa duk wani hari kan tsaron Iran, ‘yancin kai, ko hakkin mallakar kasa zai haifar da martanin da ya dace.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Majalisar Tsaron Ƙasar ta Iran  ta jaddada cewa tsaro, ‘yancin kai, da kuma haƙƙin mallakar yankin Jamhuriyar Musulunci jan layu ne kuma duk wani zalunci za a mayar da martani mai ƙarfi.

A cikin sanarwar da ta fitar, Majalisar Tsaron Kasa ta jaddada cewa: ” maimaita kalaman barazana da kalaman da ba su dace ba, wanda hakan ya saba wa ka’idojin dokokin kasa da kasa da aka amince da su.

Sanarwar ta kunshi martani bayyananne ga kalaman da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi, wanda, a cikin kalamansa, ya yi wa Iran barazana a shafukan sada zumunta da kuma a lokacin wata gajeriyar hira. Ya yi ikirarin cewa Amurka za ta goyi bayan wadanda ke bore a Iran.

A Iran, zanga-zangar data fara a makon da ya gabata bayan da ‘yan kasuwa na Tehran suka rufe shagunansu na wani lokaci don nuna rashin amincewarsu da faduwar darajar kudin kasar, wanda ya kai matsayi mafi karanci a kan dala Amurka, makiya na amfani da ita domin ingiza masu zanga zangar ta lumana.

Hukumomin Iran sun amince da matsin tattalin arziki da ‘yan kasar ke fuskanta kuma sun bayyana cewa zanga-zangar lumana halal ne, saidai

A lokaci guda kuma, sun yi gargaɗi game da yunƙurin da wasu ƙasashe ke yi na amfani da lamarin da kuma tayar da hankali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted