Kakain Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta mayar da martani kan kalaman Sakataren Baitulmalin Amurka game da takunkumai
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya mayar da martani kan kalaman da Sakataren Baitulmalin Amurka ya yi kwanan nan game da takunkumai da kuma killace tattalin arzikin Iran.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i, ya wallafa a shafin X yana mayar da martani ga Sakataren Baitulmalin Amurka -wanda ya yi magana cikin alfahari game da yunkurin musguna wa Iran ta hanyar takunkumai da killace tattalin arzikin kasar -inda “Sakataren Baitulmalin Amurka yake magana cikin alfahari game da yunkurin daukan matakin musguna wa Iran ta hanyar ‘takunkuman tattalin arziki.’ Baya ga yadda irin wadannan kalamai ke da matukar muni, kuma wannan hali yana zama shaida bayyananniya ta yadda tsarin mulkin Amurka ya kamu da muguwar dabi’ar dogaro da takunkumai.”
Baqa’i ya kara da cewa: “Duk lokacin da Amurka ta kasa ci gaba ta hanyar diflomasiyya, sai ta koma ga sanya takunkumai; kuma idan takunkuman ba su haifar da sakamako ba, sai kawai ta kara tsananta su.” Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ya ci gaba da cewa: “Wannan ba manufa ba ce; ya zama dabi’a—kuma, abin da ya fi hadari, ya zama jaraba da ta maye gurbin tunani mai ma’ana da hankali.”