Iran : Samar Da Kasashe Biyu Baya Tabbatar Da ‘Yancin Falasdinawa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya sake jaddada kin amincewa da matakin samar da kasashe biyu a matsayin samar da mafita ga rikicin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya sake jaddada kin amincewa da matakin samar da kasashe biyu a matsayin samar da mafita ga rikicin falasdinu, yana mai cewa hakan ba zai tabbatar da hakkokin Falasdinawa ba, a maimakon haka ya ba da shawarar samar da “kasa dimokuradiyya guda daya” a matsayin mafita daya tilo.

Da yake jawabi yayin taron musamman na ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, a birnin Jeddah na kasar Saudiyya da aka kira don magance cin zarafi da laifukan da Isra’ila ke yi kan al’ummar Falasdinu, Araghchi ya jaddada matsayar Iran kan Falastinu tare da bayyana goyon bayan da Tehran ke yi wa Falasdinawa a matsayin abin da ba za a iya mantawa da shi ba.

Araghchi ya kara da cewa, tare da mutunta ra’ayoyin wasu kasashe ‘yan’uwa kan batun samar da kasashe biyu, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta na kan ra’ayinta na cewa, wannan mafita ba za ta kai ga tabbatar da hakkin al’ummar Falastinu ba,” in ji Araghchi, yana mai jaddada matsayin Iran na bayar da shawarar kafa wata kasa ta dimokiradiyya wacce ke wakiltar dukkan ‘yan Falastinu.

Araghchi ya kuma yi kakkausar suka ga yunkurin gwamnatin Amurka na tilasta al’ummar Gaza kaura,” yana mai dagnata hakan da keta dokokin kasa da kasa, da yarjejeniyar Geneva ta hudu.”

Ya kuma bukaci kasashe mambobin kungiyar OIC da su aiwatar da irin wadannan matakai a matsayin wata hanya ta tursasawa gwamnatin sahyoniyawan ta dakatar da laifukan da take aikatawa kan al’ummar Gaza da sauran kasashen yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments