Iran : kasashen turai sun tafka kure na tarihi, ta hanyar goyan bayan Isra’ila

Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ta ce nahiyar turai sun tafka kure na tarihi, ta hanyar goyon bayan Isra’ila ta

Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ta ce nahiyar turai sun tafka kure na tarihi, ta hanyar goyon bayan Isra’ila ta hanyar yin watsi da sammacin kama Benjamin Netanyahu.

Esmail Baghai ya bayyana haka ne a cikin wani sako a asusunsa na X, bayan ziyarar aiki da Netanyahu ya kai kasar Hungary duk da sammacin kame shi da kotun ICC ta bayar kan laifukan yaki da cin zarafin bil adama da gwamnatinsa ta yi a zirin Gaza.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya ce : Sammacin kame jami’an gwamnatin Isra’ila da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta yi na nuni da yadda duniya ke nuna bacin rai kan kisan kiyashi, laifukan yaki, da laifukan cin zarafin bil’adama a Gaza, da kuma babbar bukatar kiyaye dokokin kasa da kasa da kuma kawo karshen rashin hukunta masu aikata munanan laifuka kan Falasdinawa.

A yammacin ranar Laraba ne Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sauka a Budapest domin gudanar da ziyarar kwanaki hudu bisa gayyatar firaministan kasar Hungary Viktor Orban.

Shugaban masu tsattsauran ra’ayi na kasar Hungary ya gayyaci takwaransa na Isra’ila duk da cewa ana zargin Netanyahu da amfani da yunwa a matsayin hanyar yaki da kuma aikata laifukan cin zarafin bil’adama da suka hada da halaka a lokacin yakin kare dangi a Gaza.

A matsayinsa na mamba a kotun ICC, ya kamata kasar Hungary ta kama Netanyahu da ya isa kasar ta tsakiyar Turai tare da mika shi ga kotu, amma haka ya bar kasar salin alin.

Kotun ICC ta yi Allah wadai da Hungary saboda kin bin sammacin kama Netanyahu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments