Jirgin yaki mallakin dakarun kare juyin juya halin muslunci a nan Iran wato IRGC ya shiga taken kudancin duniya kasa da layin Equetor a karon farko.
Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS ya bayyana cewa kataparen jirgin yakin mai suna Shahid Mahdavi ya tsallaka –Layin latitude 0% inda a karon farko ya shiga ruwan tekun kudancin duniya, da haka kuma sojojin JMI sun fadada ayyukansu a manya manyan ruwayen duniya zuwa kudancinta.
Labarin ya kara da cewa shahid Mahdavi yana da nauyin Ton 2,100 sannan tsawonsa ya kai miti 240 sai kuma fadinsa ya kai mita 27. Kafin haka dai sojojin Ruwa na kasar Iran sun yi ayyukan sintiri a yankin tun shekara ta 2023.
Shihida Mahadavi yana da kayakin aiki na zamani wadanda suka hada da rada mai hangin kusurwowi uku, makamai masu linzami wadanda ake iya cillasu daga cikin ruwa zuwa cikin ruwa ko daga ruwa zuwa sama, banda haka yana da kayakin sadarwa na zamani masu karfi.
Banda haka jirgin ruwan yakin yana da karfin hare hare wadanda suka hada da na jiragen masu saukar ungulu da kuma jiragen yakin da ake sarrafasu daga nesa wadanda suke tare da jirgin.
A shekarara da ta gabata dakarun IRGC sun gwada cilla makamai masu linzami samfurin Bilistic guda biyu daga kan jirgin, wadanda kuma suke iya zuwa tazarar kilomita 1700 daga inda aka cillasu.