Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana damuwa a kan shirin gwamnatin kasar na rage farashin mai na kwanaki 30 kacal domin saukakawa jama’ar kasar kuncin da suke ciki
Wata sanarwar da Daraktan yaɗa labaran dan takaran shugabancin ƙasar a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Frank Shaibu ya rabawa manema labarai, ta ce ragin na wata guda ba zai iy amagance matsalar da jama’ar ƙasa suka samu kan su ba.
Atiku ya ce ƴan Najeriya na buƙatar shiri na musamman da zai rage musu raɗaɗin halin da suka samu kan su na tsadar rayuwa, sabanin irin wannan mataki na wucin gadi wanda ba zai taimakawa jama’ar ƙasar ba.
wananan yana zuwa ne bayan da Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa zata ragewa ƴan ƙasar farashin mai na tsawon wata guda Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewar zata ragewa jama’ar ƙasar farashin mai na kwanaki 30 masu zuwa domin basu damar numfasawa daga tsadar da man yayi a gidajen mai.
Ƴan Najeriya sun ɗaɗe suna zargin gwamnati da nuna halin ko in kula dangane da tsadar man, a dai-dai lokacin da wasu ƙasashen duniya ke sanarwa jama’ar su mafita wajen sanya tallafi.