Malama Navi Pillay, wacce mai fafutukar kare hakkin bil’adama ce ‘yan kasar Afirka Ta Kudu ce,ta sami lambar yabo ta zaman lafiya ta “Nobel” ta wannan shekara 2026.
A baya malama Navi Pillay ta taba zama shugabar kotun duniya ta manyan laifukan wacce ta yi shari’ar kisan kiyashin kasar Rwanda, kamar kuma yadda ta rike shugabar hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD.
Bugu da kari Navi Pillay ta rike shugabancin hukumar kasa da kasa mai bincike akan Falasdinu dake karkashin mamaya a karkashin MDD.
MDD ta yaba akan bai wa tsohuwar jami’ar tata wannan lambar yabo.
Kimar wannan lambar yabon dai ta kudi ta kai Dalar Amurka miliyan 1.2 za kuma a mika mata ita ce a ranar 10 ga watan Disamba mai zuwa.