Fira minsitan kasar Guinea Bissau ya bayyana cewa har yanzu ba a kammala shirye-shiryen yin zaben shugaban kasar da na ‘yan majalisar kasar ba da ya kamata a yi a watan Disamba, saboda sabani a tsakanin majalisar soja da kuma ta shugaban da aka kawar Umar Sisko Mobolo.
Shugaban majalisar rikon kwarya ta kasar Guinea Bissau Ilídio Vieira Té ya bayyana cewa; Halin da kasar take ciki ba zai bayar da damar a gudanar da zabuka ba a lokacin da aka tsayar a cikin watan Disamba.
Fira ministan kasar ta Guinea Bissau wanda ya gana da shugaban rikon kwarya janar Hurot Inta ya ce; Har yanzu jam’iyyun siyasa ba su kammala shirinsu ba na yin zabe, domin da dama daga cikinsu ba su da cikakken tsarin shugabanci,balle kuma ace sun sun gabatar da wadanda za su tsaya takarar shugabanci a ranar 6 ga watan Oktoba ga kotun koli.
Ita kuwa jami’a a hukumar zaben kasar ta ce; Babu cikakkun kayan aiki na gudanar da zabuka. Ta kuma kara da cewa wanda yake da alhakin yanke hukunci na karshe akan lokacin yin zabukan shi ne shugaban hukumar rikon kwarya janar Horta Inta.
A baya hukumar sojan kasar ta tsayar da ranar 6 ga watan Disamba na lokacin yin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki da zummar kawo karshen lokacin rikon kwarya da mika wa fararen hula Mulki.
Sabuwar dambaruwar siyasa ta barke a kasar ne bayan da hukumar soja ta hana hambararren shugaban kasar Umar Sisco Mbalo komawa kasar.
Tsohon shuganan kasar wanda yake rayuwar hijira ya bayyana azamarsa ta son tsayawa takarar shugabancin kasa. Mahukuntan kasar sun ce yanayin yanzu bai bayar da damar da zai koma ba.