An Kashe Babban Sojan Isra’ila Guda 1 A Kudancin Labanon

sojojin isra'ila sun tabbatar da kashe babban jami'in sojinta guda 1 da kuma jikkata guda 3 a labanon

Mai magana da yawun dakarun sojin isra’ila ya sanar da kashe wani babban sojin isra’ila guda daya tare da jikkata wasu guda 3, sakamakon ba ta kashi da aka yi tsakaninsu da yan gwagwarmaya a kudancin kasar labanon

Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa  babban jami’ain sojin isra’ika ya halaka ne tare da jikkata wasu guda 3 sakamakon matsalar da aka samu na faduwar motar da take dauke da su a lokacin da suke gudanar da ayyukansu a kudancin labanon

A gefe guda kuma shugaban kungiyar larabawa don kawo canji Ahmad dibbi ya jaddada cewa lallai bangaren yan hadaka ba zau kasance a cikin gwamnati mai zuwa ba, don haka yana kira da a kada kuria sosai don kifar da gwamnatin Natanyaho, kuma yayi gargadi game da kokarin da ake yin a lalata zaben da ci gaba da siyasar da ake yi a yanzu

Daga karshe ya yi gargadi game da yunkurin da natanyaho yake yi na lalata zaben da zaa yi , domin bangaren dake mara masa baya sun fara kokarin kawo cikas akai, domin natanyaho yana son ci gaba da shugabanci ko da kuwa a gwamnatin rikon kwaryar ne

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted