Masana da fitattun mutane sun rubuta wata budaddiyar wasika, inda a cikinta suke neman a kafa gwamnatin rikon kwarya a Kamaru, saboda abinda suka kira gazawar shugaban kasar Paul Biya.
Masanan da suka haɗa da malaman jami’a da marubuta da kuma yan farar hula su 11, waɗanda mafi yawansu ke rayuwa a kasashen waje yanzu haka, sun yi kira da a gudanar da taron ƙasa wanda zai yanke hukunci game da makomar ƙasar, saboda halin da take ciki na rashin jagoranci.
Zaman lafiyar Kamaru ya dogara ne da haɗin kan yankunan ƙasar biyu, wato na masu amfani da harshen Ingilishi da kuma masu amfani da Faransanci, fitattun suka yi kira da lallai a lulubo mafita game da matsalolin tsaro da suke ƙara ƙamari, saboda barazanar da ke da ita na rugujewar kasar idan ba a sanya su cikin tattaunawar makomar Younde.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin siyasa a Kamaru ke kara kamari, inda shugaba Paul Biya mai shekaru 93 ya mamaye harkokin jagoranci a ƙasar fiye da shekaru 40 kenan.