Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya gana da jakadan Pakistan

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya gana da Omran Ahmed Siddiqui, sabon jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Pakistan a Iran, a nan birnin Tehran.

Baqaei ya gana da jakadan Pakistan

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya gana da Omran Ahmed Siddiqui, sabon jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Pakistan a Iran, a nan birnin Tehran.

A ranar Laraba, Baqaei ya wallafa a shafinsa na X cewa, “A yau na yi tattaunawa mai amfani da jakadan Pakistan, Mista Omran Ahmed Siddiqui.”

Ya kara da cewa, dangantakar dake tsakanin Iran da Pakistan ta ginu ne kan tushen tarihi mai zurfi da kuma alakar abota mai dorewa. Ya kuma bayyana cewa, Iran—kasar da ta fara amincewa da Pakistan nan take bayan samun ‘yancin kanta a shekarar 1947 ta kuduri aniyar inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu domin amfanin al’ummominsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted