Limamin Tehran: Kasashen Turai Sun Bude Yakin Duniya Akan Zaman Aure

Limamin Tehran: Kasashen Turai Sun Bude Yakin Duniya Akan Zaman Aure
limamin juma'a

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran Muhammad Jawad  Ali Akbari ya yi gargadi akan yadda kasashen turai suke fada da tsarin aure da kafuwar iyali masu nagarta, ta hanyar watsa munanan al’adu na badala da rashin kunya a tsakanin jinsin bil’adama.

Limamin ta birnin Tehran ya ce kasashen na turai sun dade suna yakar aure da tsarin iyali a fadin duniya wanda yake a matsayin “babban laifi akan jinsin bil’adama.”

Hujjatul-Islam Wal Muslimn ya kuma ce; Rayuwar da aka gina akan kame kai da kunya tana a matsayin ginshikin da rauwar zamantakewa mai ma’ana ta ginu akansu.

Limamin na Tehran ya ce yanzu an wayi gari duk duniya ta fahimci cewa kasashen turai ne suke jagorantar yada badala wanda yake a matsayin fada da ginshikin iyali.

Sai dai limamin ya kuma ce;kasashen na turai su ne na farkon wadanda suke cutuwa daga wannan yakin da su ka shelanta akan jinsin bil’adama, domin ginin iyali ya dushe a cikin kasashen na turai.

Hujjatul-Islami wal Muslimin Akbari ya ce; A halin yanzu muna cikin yanayi na gargadi da ya zama wajibi ga ‘yan siyasa da masana a cikin al’umma da iyalai su fadaka.

A wani sashe na hudubar limamin na Tehran ya yi jinjina ga matasan Iran da suke da kwazo da kuma samun lambobin yabo a yayin gasa ta kasa da kasa ta ilimi da suke zuwa na daya a shekaru uku a jere.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted