Al-Houthi: Yaki kan al’ummar yemen zai kawo karshe

Shugaban kungiyar Ansar Allah, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya bayyana a ranar Alhamis cewa yunkurin Saudiyya na karya karfin gwiwar al’ummar Yemen zai ci tura, yayin

gargadin Al-houthi ga Qatar

Shugaban kungiyar Ansar Allah, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya bayyana a ranar Alhamis cewa yunkurin Saudiyya na karya karfin gwiwar al’ummar Yemen zai ci tura, yayin da yake jawabi a bikin cika shekaru 10 da faruwar harin kisan kiyashi a Babban Zauren Taro (Great Hall) da ke Sana’a.

Ya jaddada cewa asarar da Riyadh ke yi na karuwa yayin da ta ci gaba da kai hare-hare, da kuma kakaba takunkumi.

Inda ya zargi Saudiyya da aikata laifukan yaki, tare da hadin gwiwar Amurka da “Isra’ila,” sannan ya yi gargadi ga Qatar, game da karuwar shigarta cikin yakin da ake yi kan Yemen.

Shugaban na Yemen ya kuma tabbatar da cewa sojojin Yemen na iya kai hari kan duk wani wurin da aka sa a gaba a Bahar Maliya ko Tekun Larabawa, tare da yin kira ga jama’a su fito zanga-zanga mai yawa a ranar Juma’a.

Kara karantawa: Amurka da Saudiyya sun yi kawance da ‘Isra’ila’ don yaki da kungiyoyin gwagwarmaya: Sayyed Al-Houthi

Sayyed al-Houthi ya tuna cewa harin da Saudiyya ta kai a Babban Zauren Taro da ke Sana’a a shekarar 2016 ya yi sanadiyyar mutuwar da raunata mutane kusan 1,000.

Ya bayyana cewa tun daga lokacin, kowace jiha a Yemen ta shaida “laifuka kan bil’adama da laifukan yaki da gwamnatin Saudiyya ta aikata.”

Ya zargi Riyadh da kai hari kan fararen hular Yemen da gangan “tare da abokan kawancenta na Amurka da Isra’ila,” sannan ya yi watsi da manufarta ta tilasta wa ‘yan Yemen su mika wuya inda ya kwatanta hakan da burin da mafarkin da ba zai taba tabbata ba.

Ya jaddada cewa asarar da Saudiyya ke yi “na ci gaba da karuwa yayin da ta ci gaba da kai hare-hare da kuma kakaba takunkumi.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted