A wata sanarwa mai lamba 18 da IRGC su ka fitar sun bayyana kai hari akan wani babban jirgin Ruwan dakon gas, tare da dora alhakin abinda yake faruwa akan sojojin Amurka masu wuce gona da iri.
Sanarwar ta dakarun kare juyin musulunci ta kuma ce; jirgin Ruwan da aka kai wa harin, shi ne “Nv-Sunshine” yana dauke da gas ne nau’in LPG, wanda kuma mallakin kamfanin Nat-Vit ne.
Haka nan kuma ta ce alhakin hakan yana wuyan Amurka da take yaudarar wasu kamfanonin sufurin jirgin ruwa bayan ta karbi cin hanci da rashawa a wurinsu.
Dama dai tun da fari dakarun kare juyin musuluncin sun fitar da gargadi dake cewa; Duk jirgin Ruwan da ya keta doka zai fuskaci ladabtarwa a ko’ina yake a wannan yankin ba sai ta mashigar Ruwan Hurmuz ba kadai.
Rundunar ruwa ta dakarun kare juyin musulunci na Iran ta sanar da cewa; duk wani jirgin ruwa wanda yake bi ta barauniyar hanya ba wacce Iran ta Shata ba,to zai fuskanci ladabtarwa a ko’ina yake a cikin wannan yankin.
A yau Juma’a ne dakarun IRGC su ka fitar da sanarwa wacce ta kunshi gargadi ga jiragen Ruwan da suke kokarin shiga ta wata hanya ba wacce aka Shata ba a mashigar Ruwan Hurmuz, tare da jaddada cewa; Daga yanzu duk wani jirgin da zai saba doka a ko’ina yake a cikin wannan yankin ba, to zai fuskanci ladabtarwa babu makawa.