Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya tabbatar da cewa, Isra’ila da Amurka ne suka bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa bayan da suka fuskanci martani mai tsanani a lokacin da suka kaddamr da hare-hare kan kasar Iran.
A yayin da yake karbar bakuncin babban kwamandan rundunar tsaron kasar a Afirka ta Kudu, Janar Hatami ya ce, hukumomin Isra’ila da Amurka sun yi amfani da dukkan karfinsu wajen kai wa Iran hari, amma sun kasa cimma burinsu.
Har ila yau, ya bayyana matakin da Afirka ta Kudu ta dauka na shigar da kara kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a kotun kasa da kasa a matsayin wata babbar Jarunta, yana mai jaddada cewa tarihi zai tabbatar da wannan muhimmin mataki.
Har ila yau, Laftanar Janar Hatami ya bayyana cewa, dukkanin kasashen biyu suna da Akida ta adawa da mulkin mallaka, yana mai cewa: Matukar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Afirka ta Kudu suna da kyakkayawan hadin gwiwa da juna, to kuwa tabbas za su yi tasiri wajen mara baya ga al’ummomin da ake zalunta, da kuma kalubalantar babakere na ‘yan mulkin mallaka.
A nasa bangaren, kwamandan rundunar tsaron kasar a Afirka ta Kudu, Laftanar Janar Rodzin Mafwania, ya ce ziyarar Iran a yau ba ziyarar soji ba ce kawai, a’a sakon siyasa ne, kuma ta zo a daidai lokacin da ya dace mu bayyana ra’ayinmu ga al’ummar Iran masu son zaman lafiya.
Kuma ya ci gaba da cewa: “Muna tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan wadanda ake zalunta da kuma wadanda aka raunata a duniya, shi ya sa muka shigar da kara a gaban kotun kasa da kasa domin hukunta wadanda suka aikata laifukan yaki.”