Iran da Saudiyya sun jaddada wajabcin kara karfafa  dangantakasu

Ministocin harkokin wajen Iran da Saudiyya sun tabbatar da aniyar kaasashensu na ci gaba da kara azama domin bunkasa alakoki a tsakaninsu a dukkanin bangarori.

Ministocin harkokin wajen Iran da Saudiyya sun tabbatar da aniyar kaasashensu na ci gaba da kara azama domin bunkasa alakoki a tsakaninsu a dukkanin bangarori.

Wannan dai na zuwa ne a yayin ganawar da ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araghchi da takwaransa na kasar Saudiyya Faisal bin Farhan suka yi ne a wannan Juma’a a gefen taron gaggawa karo na 20 na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi a birnin Jeddah.

A yayin wannan ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan matsayin dangantakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma masarautar Saudiyya, tare da jaddada aniyar kasashen biyu na ci gaba da fadada hadin gwiwa tsakaninsu.

Bangarorin biyu sun kuma yi nazari kan halin da ake ciki a kan batutuwa daban-daban da suka shafi yankin, da ma sauran batutuwa na kasa da kasa, tare da jaddada wajibcin yin hadin gwiwa a tsakanin dukkanin kasashen musulmi wajen tinkarar kalubale dangane da batun Palastinu da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta mamaye, da kuma hana aiwatar da makarkashiyar da ake shiryawa da nufin share batun  Palastinu, ta hanyar tilastawa al’ummar Gaza yin gudun hijira daga yankinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments