Kasashen Iran da Iraki sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro ta hadin gwiwa a wannan Litinin, dangane da tabbatar da tsaron kan iyakokin kasashen biyu, a ziyarar da babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya kai kasar Iraki.
Larijani da mai baiwa gwamnatin Iraki shawara kan harkokin tsaro, Qasim al-Araji, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a karkashin jagorancin firayi ministan Iraki Mohammed Shia al-Sudani.
A yayin ziyarar tasa a Bagadaza, Larijani da tawagarsa sun gana da shugaban kasar Iraki Abdul Latif Rashid, da kuma firayi minister al-Sudani da kuma shugaban majalisar dokokin kasar.
A yayin ganawar tasu, Rashid da Larijani sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka shafi yanking abas ta tsakiya, da kuma na kasa da kasa, inda suka jaddada muhimmancin ci gaba da tattaunawa mai ma’ana a tsakanin kasashen yankin, don warware rikice-rikice da kuma yin aiki don tabbatar da ka’idojin mutunta juna da rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida, a cewar wata sanarwa da fadar shugaban kasar Irakin ta fitar.
Rashid ya jaddada “zurfin dangantakar tarihi da cin moriyar juna a tsakanin Iraki da Iran,” yana mai bayyana muradin kasarsa na samar da tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta hanyar da ta dace da al’ummominsu da kuma karfafa tsaro da zaman lafiyar yankin.
A nasa bangaren, Larijani ya bayyana jin dadin kasarsa ga matsayin kasar Iraki na goyon bayan tabbatar da tsaron yankin da kuma rawar da take takawa wajen kusanto da ra’ayoyin bangarori daban daban.
Shi ma firaministan kasar Iraki ya tabbatar da “kokarin da Bagadaza ke yi na raya dangantakar da ke tsakaninta da Tehran da karfafa dangantakar abokantaka mai inganci a matakai da fagage daban-daban, bisa maslahar al’ummomin kasashen biyu.”
Al-Sudani ya bayyana matsayin kasar Iraki na kin amincewa da kai hare-haren da Isra’ila ta yi a kan Iran, sanann kuma ya bayyana goyon bayan Bagadaza ga tattaunawar Amurka da Iran.