Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi a tattaunawarsa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Cuba Bruno RodrÃguez ya bayyana cewa bangarorin biyu sun kara karfafa dankon zumunci a tsakaninsu. Kuma sun yi allawadai da gwamnatin kasar Amurka kan takurawa kasashen biyu da take yi.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya ce ministocin biyu sun yi allawadai da yadda Amurka yake takurawa kasashen duniya wadanda basa daswa da ita, musamman abinda ta aikata a kasar Venezuela a ranar Asabar da ta gabata, inda ta sace shugaban kasa Nicolas Madoro da matarsa Cilia Flores a cikin fadar shugaban kasa.
Kasashen Iran da Cuba dai suna fuskantar takunkuman tattalin arziki mafi muni daga kasar Amurka, na shekaru aro-aro amma suka ki mika kai ga bukatunta. Ministocin sun bayyana cewa aikin sojen da gwamnatin kasar Amurka ta yi a kasar Venezuela a ranar Asabar da ta gabata keta dokokin kasa da kasa ne, kuma hakan ya nuna duniya ta dawo cikin dokokin daji, inda mai karfi kawai yake da iko a kan sauran